Darektan sadarwa na kungiyar Asante Kotoko ta kasar Ghana Lauya Sarfo Duku, ya ce kungiyar na shirin kafa tarihi a Zambia inda take niyar lallasa kungiyar Nkana FC ta Zambia a cikin gidanta, a gasar cin kofin zakarun Afrika ta CAF Confederation.
Asante Kotoko mai lakabin Porcupine Warriors, zata kara da Nkana FC ne a wasa na uku na matsayin rukuni a wannan gasar a can Zambia, inda babu wanda ya taba cin Nkana FC tun lokacin da ta fara shiga wannan gasa a shekarar 1976, da ake kiranta da Rhokanna United, shekaru 43 da suka shude.
Amma shi kuwa Lauya Duku ya ce yana kyautata zaton Asante Kotoko zata kafa tarihi na zama kungiya ta farko da zata fara bawa Nkana FC kashi a cikin gidanta.
Shima mai horar da ‘yan wasan Nkana FC Beston Chambeshi ya ce yana nan yana shirya dabarun tinkarar yadda zai takawa Asante Kotoko burki a cikin wannan gasa.
Nkana FC zata amshi bakuancin Asante Kotoko a wasa na uku, a filin wasa na garin Kitwe a ranar Lahadi a gasar cin kofin zakarun Afrika.
Facebook Forum