Jami’an hukumar zaben Nijeriya sun yi alkawarin gudanar da zaben wannan shekarar cikin adalci da inganci, kuma sun kawo wasu salon kada kuri’a da nufin magance magudi da kuma kawar da rudami.
Alhamis da ta gabata ce, wata jam’iyyar hamayya a Nigeria dake yankin Naija Delta mai arzikin man fetur ta zargi jami’an tsaro da tsangwama bayan an tuhumi wani wakilinta da laifin cin amanar kasa da kisan kai.
An zargi John James Akpanudoedehe, dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom da laifin cin amanar kasa a makon jiya bayan wani tashin hankali tsakanin magoya bayan jam’iyyarsa ta CAN da na PDP. An bada belinsa ran Alhamis, to amman sai nan da nan kuma aka sake kama shi bisa laifin kisan kai. Magoya bayansa sun ce zargin da ake masa nada alaka da siyasa.