Ina tunanin daukar ciki. Ta yaya zan kula da kaina?
Ya kamata ki fara kula da kanki kafin ki dauki ciki. Ana kiran wannan kula da lafiyar jiki kafin daukar ciki. Yana nufin sanin yadda yanayin lafiyar jiki da hadarinshi zai iya shafar jariri dake ciki idan kika dauki ciki. Misali, wadansu irin abinci, da halayya, da magunguna suna iya zama da illa ga jariri- tun kafin a dauki cikinshi. Wadansu cututuka kuma suna iya zama da illa ga daukar ciki.
Ki tuntubi likitanki kafin ki dauki ciki domin sanin abinda ya kamata ki yi domin ki shirya jikinki. Ya kamata mata su yi shirin daukar ciki tun kafin su dauki ciki. Ya kamata mata su ba kansu a kalla watanni uku kafin su dauki ciki.
Muhimman abubuwa da ya kamata kiyi guda biyar kafin daukar ciki sune:
1. Ki sha maganin folic acid mikrogram 400 zuwa 800 (400 to 800 mcg or 0.4 to 0.8 mg) kowacce rana na tsawon akalla watanni uku kafin ki dauki ciki, domin gudun kada a haifi jaririn da wata illa a kwakwalwa ko kuma kashin gadon bayanshi. Zaki iya samun sanadarin folic acid a cikin wadansu abinci. Sai dai yana da wuya ki sami dukan folic acid da kike bukata daga abinci kadai. Shan sinadarin vitamin da kuma folic acid shine hanyar da tafi dacewa da kuma sauki ta tabbatar a cewa kin sami sinadarin isasshen.
2. Ki daina shan taba da giya. Ki nemi taimakon likita.
3. Idan kina da wata cuta, ki tabbata kina samun magani. Wadannan cututuka sun hada da asma da ciwon suga, da bakin ciki, da hawan jinni da mummunar kiba, da cutar makoshi, ko kuma farfadiya. Ki tabbata kin yi dukan rigakafin da ya kamata.
4. Ki bayyanawa likita dukan magungunan da kike amfani da su. Wadannan sun hada da sinadarin gina jiki ko kuma magungunan gargajiya. Wadansu magunguna suna da illa ga daukar ciki. Haka kuma daina shan magungunan da kike bukata yana da illa.
5. Ki nisanci abubuwa masu guba a wurin aiki ko gida da zasu iya zama da illa gareki. Ki nisanci sinadarin harhada magunguna ko kashin mage da na bera.