Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana wasu matakai da za su iya kai kungiyar ga samun nasara a jerin manyan kungiyoyi hudu don samun lashe kofin bana.
Kungiyar ta Arsenal ta bi sahun Chelsea a matsayi na hudu da maki bakwai, bayan da Chelsea ta kara jan ragamar kungiyar a kan abokiyar hamayyarta ta Tottenham Hotspur da ci 2-1 a ranar Asabar.
Arsenal dai ta dare tsakiyar tebur bayan nasarar da ta yi a wani karon batta da ta yi da Everton a gidanta a ranar Lahadi. Tsohon kocin Wenger wanda ya yi hasashen cewa yana da yakinin kungiyar za ta iya zama cikin jerin kungiyoyi hudu da zasu kai labari.
Ya kuma shaida wa BeIN Sports cewa "Dukansu sun samu dama saboda suna ganin manyan kungiyoyi uku sun nisanta kansu da sauran wasannin, wasu sun matsa sama, wasu kungiyoyi kuma a cikin manyan su shida, sun yi watsi da matakin nasu." ya kara da cewa “Muna da maki 33 da muke nema, idan ka samu maki 22-25, kana da dama."
Facebook Forum