Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke kasar Ingila, ta yi bikin cika shekara 21 da sayen tsohon dan wasan Najeriya Nwankwo Kanu.
A ranar Laraba da ta gabata tsohon dan wasan na Arsenal da Super Eagles Kanu ya cika shekaru 21 da sanya hannu a kungiyar Arsenal da ta saye shi daga Inter Milan ta kasar Italiya.
A yayin bikin, Arsenal ta wallafa faifan Bidiyo a shafinta na sada zumunci Twitter na kwallaye biyar da Kanu ya ci mafiya kyau a lokacin yana dan wasa.
A ranar 15 ga watan Janairun 1999, Arsenal ta saye shi akan kudi fam miliyan £4m karkashin jagorancin kocinta Arsene Wenger.
Kanu dan shekara 43 da haihuwa, ya buga wasanni 119, wa Arsenal ya zira kwallaye 44, kafin daga bisani ya canza sheka zuwa West Bromwich Albion a shekara ta 2004.
A lokacin da yake Arsenal, ya lashe kofin Premier sau biyu sai kofin Kalubale na FA Cup, da kuma Community Shield sau daya.
Facebook Forum