WASHINGTON, D.C. —
A yunkurinsa na ganin ya farfado da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, sabon kocin kungiyar Mikel Arteta ya sanya wasu 'yan kwallon Najeriya cikin manyan 'yan wasan kungiyar Arsenal.
'Yan wasan, da suka hada da Tolaji Bola da James Olayinka, dukansu sun yi atisaye tare da manyan 'yan Arsenal ranar Lahadin da ta gabata.
Bayan haka kulob din na shirye-shiryen bada dan wasanta Granit Xhaka ga kungiyar Leicester City, zata kuma kara da kudi don karbo dan wasan tsakiya na Leicester, mai suna Wilfried Ndidi.
Wilfred Ndidi shi ma dan Najeriya ne kuma tauraruwarsa na haskakawa a gasar firimiyan Ingila. Kungiyoyi daban-daban sun nuna sha'awar daukar shi musamman na nahiyar Turai.
Facebook Forum