Nan ba da jimawa ba kamfanin Apple zai kaddamar da sababbin wayoyin sa na iPhone 12, wanda zasu zo cikin lau’nuka daban-daban da suka kai har 6. Kana kamfanin na shirin dawo da tsohuwar wayar shi ta iPhone SE, wanda aka inganta ta da wasu sababbin manhajoji.
Sabuwar wayar ta iPhone 12 zata shigo kasuwa a watan Satumbar 2020, sabuwar waya zata zo dauke da manhaja ta 4G da 5G, domin kuwa sabon cigaban 5G zai sa wayar tayi tsada kuma bazata yi aiki a wasu kasashen duniya ba saboda karancin tsarin 5G.
Sabuwar wayara iPhone 12, za’a rage mata girma ta yadda zata dinga shiga aljihun mutane cikin sauki, kuma kamfanin ya raba nau’ukan wayar gida shida da suka hada da ta farko iPhone 12 4G: 6.1-inci LCD, kyamara biyu, ta biyu iPhone 12 Pro 4G: 5.4-inci OLED, kyamara biyu.
Ta uku iPhone 12 Pro 5G: 5.4-inci OLED, kyamara biyu, sai ta hudu iPhone 12 Pro Plus 4G: 6.1-inci OLED, kyamara uku, 3D tana iya daukar murya da fatar jikin mai ita, ta biyar kuwa iPhone 12 Pro Plus 5G: 6.1-inci OLED, kyamara uku, ta kkarshe kuwa it ace iPhone 12 Pro Max 5G: 6.1-inci OLED.
Facebook Forum