Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta shirya tsaf don zaben wanda zai wakilci jam’iyyar a zaben shugaban kasa da za a yi a badi.
Bayan kai ruwa rana da aka yi a ranar Litinin, a karshe rahotanni sun yi nuni da cewa gwamnonin jami’yyar sun tantance mutum biyar da za su shiga zaben.
‘Yan takara da gwamnonin jam’iyyar suka tantance su biyar sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, tsohon gwamman Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi da gwamnan Ebonyi Dave Umahi.
A ranar Litinin shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan a matsayin wanda jam’iyyar ta zabe.
Sai dai fadar shugaban kasa ta nesanta kanta sanarwar Adamu, inda shugaba Muhammadu Buhari ya ce fadarsa ba ta tsayar da dan takara daya tilo ba.
Tun a baya dai gwamnonin jihohin arewa a jam’iyyar, sun amince a ba dan kudu tikitin takarar shugaban kasar, matakin da bai yi wa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da wasu mambobin jam'iyyar dadi ba.
Tuni filin Eagle Sqaure, inda za a yi zaben, ya sha kwalliya, kuma rahotanni ma na nuni da cewa har an kammala tantance daliget ko wakilan da za su yi zabe.
Daliget 2, 322 ne za su yi zaben kamar yadda rahotanni suka nuna.