WASHINGTON, DC —
Jam’iyyar ta APC dai, ta sha fama da rikicin cikin gida, da ya hana a gudanar da zaben shuwagabannin nata a baya.
Barrista Usman Dalhatu, shine shugaban kwamitin shirya zaben, da uwar jam’iyyar ta APC ta tura daga Abuja, wanda yayi bayanin wanda yayi nasara daga cikin ‘yan takara 8 da suka fafata wajen neman kujerar.
“To alhamdulilLahi, kamar yadda aka sani, mun fara zabe tun jiya da wajen karfe 10 na safe, yanzu kuma mun kammala tattara wannan sakamako na zabe da aka yi,” a cewar Barrista Dalhatu. “Amma wannan kammala zaben da muka yi, ya nuna cewa Injiniya Muhammad Jibrin Adamu shine yaci zabe, da kuri’a 1142.”
Shugaban riko na jam’iyyar mai barin gado a Jihar Neja, Senata Ibrahim Musa, ya bayyana gamsuwa da yadda aka shirya zaben, sannan yace rikicin dake cikin jam’iyyar, ba wani abun damuwa bane.
A yanzu dai, kwamitin shirya zaben ya bayarda mako guda, ga masu korafe-korafe akan zaben, daga ranar Lahadinnan.