Hatsarin da motar dakon mai tayi a daren jiya Alhamis zuwa safiyar yau Juma’a, ya janyo matsalar kwararar mai zuwa tafkuna, da rijoyi da kogunan dake zagayen yankin. Don haka ruwan sha mai lafiya da tsafta na neman ya gagari al’ummar dake zaune a yankin Zamfara da Sokoto dake makwabtaka da ita.
Wata babbar matsalar kuma itace jami’ai sun koka game da rashin kayan aiki da fasahar tace ruwan daga man dake gurbata ruwan. Domin ta haka ne kadai za’a iya hana sake afkuwar gurbacewar ruwan sha nan gaba.
Mutari Lugga, shine Kwamishinan Ma’aikatar kare muhalli a jihar Zamfara, ya kokarta isa wurin da hatsarin ya faru inda mai ya rika tsiyayewa zuwa cikin ruwa da Asubahin yau Juma’a. Yace yaga wasu mutane a tsaye kusa da wurin da hatsarin ya abku, amma jami’an hakar gwal ne wanda shine gadon bayan tattalin arzikin jihar Zamfara, amma babu abinda zasu iya yi sai zuba ido, litar mai dubu 33 na ta kwarara zuwa ruwan tafkuna da rijiyoyi.
Mouktari Lugga sai ya kara da cewa:matsalar kam babbace, domin yanzu ana tsakiyar lokacin damuna. Lokacin da ruwan tafkuna da koguna ke cika suna batsewa har su rika kwaranya, gashi kuma bamu da wata fasahar yadda za’a iya bullo domin kauda wannan matsala ta kwaranyar ruwa.