Jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da nuna damuwar su dangane da yunkurin gwamnatin kasar nayin sauye sauye a kudin tsarin zaben kasar, wanda suke ganin cewar baza’a yi musu adalci ba, hakan yasa kungiyar kasashe rainon Faransa, OIF shiga cikin lamarin don ganin yadda za’a magance matsalar.
Kakakin kungiyar OIF Dr. Adalu Rubaid, wanda yaja ragamar tattaunawar da kungiyoyin ‘yan adawa ya bayyanar da cewar, sun ja hankalin jam’iyyun da su tsaya akan gaskiyar su da kuma tunanin cewar abun da kowa ya fada shi zaiyi, don kuwa babbar matsalar siyasar Nijar itace rashin gaskiya da amana a yadda ake gudanar da siyasar.
Ya kara da cewar sun ja hankalin mahukunta da su maida hankali wajen ganin abun da suka ayyanar sun tsaya akanshi, babban burin su a cikin wanna tafiyar shine a kawo karshen duk wasu rashin jituwa a tsakanin jam’iyyu ganin yadda zabe ke kara karatowa.
A bangaren jam’iyyun adawa kuwa ta bakin kakakinsu Anibu Sumaila, suna ganin cewar sabon garanbawul din da ake kokarin yiwa kundin tsarin zaben ba zai haifar da da mai idoba musamman ga jam’iyyun adawa, suna kira da a koma kan tsohon tsarin, kuma suna jan hankalin mahukunta da cewar, wannan matsalace da take ta cikin gida don haka babu bukatar sai an dauko wasu daga wajen don magance ta, suna iya magance ta a tsakanin su.
Don Karin bayani sai ku saurari rahoton wakilin shashen Hausa na Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum