Wani bincike da hadakar kungiyar kare hakkin dan adam tare da hadin gwuiwar wasu yan jarida a jihar suka gudanar na nuni da cewa jami’an dake shingayen kan ci zarafin wadanda suka tsare ta hanyar dauri da igiya da kuma karban kudade,kamar yadda muka tarar a daya daga cikin wajen binciken dake Mayo-Lope.
Baya dai ga matafiyan da aka tsare,haka nan an ji ta bakin wani direba,wanda yace ana tatsansu.
Kamar yadda muka tarar, wani jami’in dan sanda da suka yiwa lakabi da Roni da kuma wasu yan banga,suke kula da wannan waje,ko da yake sai da muka kai ruwa rana da su a wannan waje da suka tsare matafiyan.
Wannan batu dai ya tada hankulan yan rajin kare hakkin dan adam a jihar inda Barrister M.B Mustapha ke kira ga gwamnatin tarayya da ta binciki lamarin na ko shin gwamnatin jiha na da izinin hana wani shiga wata jihar?
Kawo yanzu rundunan yansandan jihar ta yi gum da bakinta,game da zargin da ake yi na cewa da hannunta a wannan lamari, domin duk kokarin ji daga bakin kakakin rundunan abun ya citura inda wata majiya tace ba ya gari,an yi masa mutuwa,to sai dai kuma gwamnan jihar Arch.Darius Dikson Isiyaku ya tabbatar da lamarin .
Gwamnan ta bakin hadiminsa ta fuskar harkokin yada labarai Mr Sylvanus Giwa,yace sun dau wannan mataki ne don hana wadanda ya kira bata gari shigowa.
Facebook Forum