Tsohon shugaban cocin darikar Katolika na kasar Kamaru, Kiriten Tumi, ya kira gwamnatin kasar ta yi kokari ta inganta matakan kare hakkin bil Adama a bangaren 'yan aware da ke amfani da Ingilishi a kasar.
Ya yi kiran ne saboda yadda jami'an tsaro ke musgunawa mazauna jihohin biyu da ke yankin a kasar ta Kamaru.
Sai dai kakakin gwamnatin kasar kuma ministan sadarwa, Isah Ciroma Bakari, ya musanta zargin cikin martanin da ya mayar wa Kiriten Tumi.
A cewar shi, suna ba Kiriten Tumi girmansa saboda suna ganinsa a matsayin daya daga cikin iyayen kasa.
Ya kara da cewa su basa take hakkin kowa amma suna kare 'yan kasarsu ne daga harin ta'addanci.
A cewar ministan duk 'yan kasar Kamaru basa bukatan a raba ta ko a bangaren Ingilishi ma saboda wai, kashi 90 na al'ummar kasar na son zaman lafiya.
Ya kara da cewa, 'yan tsiraru ne kawai ke ta da hankalin kasar ko kuma yakin kabilanci.
Saurari sharhin da Malam Zakari, masanin siyasar kasar ta Kamaru ya yi a wannan rahoto na Muhammad Awal Garba ya hada:
Facebook Forum