Hatsarin ya auku ne a ranar Laraba, sa'adda tankar da ke dauke da man fetur ta fadi ta kuma kama da wuta a garin Lokoja, lamarin da yayi sanadiyyar konewar mutane kimanin 30, mafi akasarinsu yara 'yan makaranta.
Kwamishinan Watsa Labarai na jihar ta Kogi Kensley Panwo, ya ce lamarin babban abin damuwa ne, ya kuma ce "gwamnati za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan al'amari."
Hatsarin motocin dakon mai a Najeriya abu ne da manazarta suka ce ya zama ruwan dare a kasar, lamarin da direbobin tanka din ke ta'allakawa da rashin kyan titunan kasar.
Faruku Muhammad Kawo, mataimakin shugaban kungiyar direbobin tanka a jihar Naija, ya ce rashin kyawawan hanyoyin mota ne ke haddasa yawan hatsura, musamman a Arewacin Najeriya.
Ya ce rashin ingantattun hanyoyi ke sanya direbobin daukar lokaci mai tsawo akan hanya, wanda kuma hakan kan haifar da rashin isasshen bacci, lamarin da kan jefa da yawansu a cikin hadurra.
A makon da ya gabata ma kungiyar direbobin ta yi barazanar dakatar da aikin jigilar mai zuwa Arewacin Najeriya, sadoda rufe wata hanya da gwamnatin jihar Naija ta yi saboda lalacewarta.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari:
Facebook Forum