Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zagaye Na Biyu A zaben Kasar Jamhuriyar Benin


Katunan Zabe a Jamhuriyar Benin
Katunan Zabe a Jamhuriyar Benin

A yau ne ake sake zabe zagaye na biyu a jamhuriyar Benin kuma Sahabu Imam Aliyu ya samu damar tattaunawa da wani dan kasuwa kuma dan siyasa Alhaji Amadu Cotounou.

Da farko ya fara yiwa Sahabun bayani ne game da fitowar Jamaa, ga kuma abinda yake cewa.

‘’Wato akwai inda aka bude karfe 7 akwai inda aka bude 7:15 akwai kuma 7:30 an bude su akan lokaci kuma ba’a samu wani matsala ba, har zuwa wannan lokacin.’’

Da kuma Sahabun ya tambaye shi ko yaya fitan jamaa ida an kwatanta da zaben farko anan ko sai Alhaji Amadu ya amsa da cewa.

‘’Lallai dai akwai matsala game da wannan kuma ince babba saboda mutane basu fito ni ina cikin babban birnin kasar wato Cotonou, mu mun fita kuma munyi zabe kuma munyi zabe, munga cewa mutane basa fitowa.’’Sai kuma Sahabun ya sake tambayar sa ko me yasa yake ganin mutane basu fito ba?

‘’Yace dalilin dai an samu ba zata ne domin ko wadan da akayi zaton zasu zo zagaye na biyu bashi ne yazo ba.

Ga ci gaba da tattaunawar tasu 3’16

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

XS
SM
MD
LG