A jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar, zaben Gwamna za a kammala inda fafatawa ta fi zafi tsakanin Gwamna mai ci Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP da ‘yar takarar APC Sanata Aishatu Dahiru Binani.
Hukumar zabe ta INEC ta ayyana cewa zaben bai kammala ba a watan Maris, bayan da aka gano an samu sabani a adadin kuri’u.
Fintiri ya samu kuri’a 421, 524 Binani kuma ta samu 390, 275.
A ranar 18 ga watan Maris aka yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihar bayan da aka dage shi daga ranar 11 ga watan Maris.
A jihar Kebbi ma, za a yi zaben a sassan jihar da dama. A zaben farko, APC ta samu kuri’a 388,258, sai PDP da ta samu kuri’a 342, 980.
INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba bayan da aka gano cewa an yi rikici a wasu jihar sannan an yi arangizon kuri’u.
A jihar Adamawa, bayanan da shafin yanar gizon INEC ya wallafa sun nuna cewa za a yi zabe a rumfuna zabe 69, wadanda ke da jimullar masukada kuri'a 37, 706.
A Kebbi kuwa, a rumfunan zabe 142 za a yi kada kuri'a, kuma ana sa ran masu zabe 94,209 ne za su fita kada kuri’a.
Baya ga wadannan zabuka a jihohin Adamawa da Kebbi, akwai zabukan ‘yan majalisun tarayya da na ‘yan majalisun jihohi da ba a kammala ba a wasu jihohin Najeriya da suka hada da Sokoto da Kano.