Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana tuhumar wadansu 'yan Najeriya biyu da alaka da al-Qaida


Wani hari da mayaka suka kai
Wani hari da mayaka suka kai

Wata kotu a Najeriya ta tuhumi wadansu mutane biyu da laifin alaka da kungiyar ta’addanci ta al-Qaida

Wata kotu a Najeriya ta tuhumi wadansu mutane biyu da laifin alaka da kungiyar ta’addanci ta al-Qaida, da kuma niyar daukar sababbin membobi da kaisu Yemen.

Yan Najeriyan, Olaniyi Lawal da Luqman Babatunde, sun musanta aikata laifin jiya alhamis, a wata kotun tarayya dake Abuja.

Masu shigar da karar suna zargin mutanen biyu da karbar dalar Amurka dubu shida daga kungiyar al-Qaida dake yankin Larabawa, da nufin daukar sababbin membobi da sufurinsu. Kungiyar kishin Islaman da aka kafa a shekara ta dubu biyu da tara, tafi karfi a Saudiya da kuma Yemen.

Kwararru sun bayyana cewa, ainihin kungiyar ta al-Qaida da Osama bin Laden ya kafa, tafi karfi a tsakanin al’ummomin da take, inda take haddasa asarar rayuka da kaddarori fiye da kasashen yammaci.

Sai dai al’ummar kasa da kasa na sa ido kan kungiyar al-Qaida dake yankin larabawa, sabili da yunkurin kaiwa Amurka da wadansu kasashen yammaci hare-haren bom da kungiyar ta yi da basu yi nasara ba.

XS
SM
MD
LG