Sabon jirgin saman samfarin Boeng BBG, gwamnati ta yanke shawarar sayenshi ne bisa ga la'akari da matsala da kuma tsufar da tsohon jirgin da shugaban ke hawa yayi. An sayi tsohon jirgin ne tun sama da 1970.
Kimanin sefa samada da miliyan dubu ashirin ne gwamnatin ta ware domin sayen jirgin wanda adadin mutanen da yake dauka basu wuce ashirin da hudu ba kawai.
A cikin jirgin akwai wurin hutawa da kwanciya da wurin zama domin aiki koko wurin yin taro da sauransu wanda hakan ke cewa jirgi ne irin na zamani.
Kanal Isa Bulama Zanna Bukar shi ne kwamandan jirgin saman shugaban kasa a jamhuriyar Niger yace jirgin na iya zuwa New York daga Niamey. Yana iya zuwa China amma sai an sauka wani wuri a sha mai.
Majalisar dokokin kasar tayi wani zaman gaggawa domin duba kasafin kudin kasar inda 'yan adawa suka gano cewa gwamnatin ta lakume kudade domin sayen sabon jirgin. 'Yan adawa sunce an yi hakan ne ta wata barauniyar hanya ba tare da saninsu ba. Tijjani Abdulkadiri madugun 'yan majalisa na adawa yace majalisa ta ba gwamnati izinin tura sojoji zuwa kasar Mali lamarin da yasa ta kawo kasafin kudi miliyan dubu ashirin da daya na cewa za'a sayawa soja kayan aiki. Daga baya kuma sai gwamnati ta nemi kashe miliyan bakwai wai domina yiwa jirgin shugaban kasa rumfa.
Ministan tsaron kasar ya mayar da martani akan kalamun 'yan majalisar yace adawa ce kai. Yace a barsu su yi magana. Aikinsu ne na adawa. Yace su a bangaren gwamnati sun san abun da su keyi kuma zasu yiwa 'yan kasar aiki. Nan da shekara biyu zasu koma neman zabe. Idan 'yan kasar sun ji dadain abun da suka yi sai su zabesu idan kuma basu ji sai su koresu daga mulki.
Masu fashin baki suna ganin lokaci bai yi ba da za'a ware makudan kudi domin sayen jirgin sama idan aka yi la'akari da halin talauci da fatara dake damun a'ummar Niger su sama da miliyan goma sha bakawai. Wasu kuma suna ganin lokaci yayi na sake wa shugaban kasa sabon jirgi.
Ga rahoton Abdullahi Manman Ahmadu.