Darektan cibiyar yaki da cutar kanjamau na Najeriya Farfesa John Idoko, ya bayyana cewa, yammata sun fi fuskantar hatsarin kamuwa da cutar kanjamau idan ba a tarbiyantar da su ba.
Darektan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da wata mujallar kiwon lafiya a birnin Ikko. Bisa ga cewarshi, ‘yan matan da suka ballaga suna cikin hatsarin kamuwa da cutar kanjamau sabili da irin yanayin da suke girma ciki da al’ada da ke sa su yi jima’I mazan da suka girme su.
Idoko yace wadansu camfe-camfen a kasar suna sa ‘yammatan da suka balaga su yi jima’I da maza dabam dabam, ko su ki bayyana ra’ayinsu na mu’amala da jinsi daya, wanda bisa ga cewar darektan yana kara yada cutar kanjamau.
Farfesa Idoko ya bada shawarar sa ilimin mutumtaka a darusan makarantar jami’a da sakandare domin ilimantar da matasa yadda zasu yanke shawarar da zata taimake su da kare lafiyarsu.
Darektan ya bayyana damuwa ganin samar da wannnan damar zata iya budewa wadansu matasa kafar shiga ayyukan assha, ya kuma shawarci al’umma su bada gudummuwa domin cimma burin kare rayuka da lafiyar ‘yammata.