A baya an yi yinkurin aikin madatsar ruwan Kafin Zaki dake jihar Bauchi, aikin da mutanen jihar Yobe mai makwabtaka da jihar suka yi ta adawa da shi bisa fargaban rasa ruwan dake isa yankunansu.
Ministan albarkatun Ruwan Najeriya Injiniya Suleiman Hussaini Adamu, ya shaida cewa ana takaddama akan batun madatsar ruwan Kafin Zaki. Ya fadi cewa ya tararda muhawarar da akayi akan amincewa da kawo kwararru su yi nazari akan illar wannan aikin ga al’ummar dake yankin jihar Yobe, amma bai gamsu da rahoton da ya samu ba. a saboda haka yanzu za a sake yin nazarin batun ta yadda gwamnatocin Bauchi, da Yobe, da Jigawa zasu yarda su amince a cewar ministan.
Tsohon babban sakataren dake raya kogin Kwara, Dan masanin Fika, Alhaji Bababa Abba shi ma yace akwai bukatar daukar matakin tattaro wakilan wadannan jihohin don kaucewa fadawa wata matsala a gaba.
Shi kuma Injiniya Dr. Hussaini Hassan, kwararre akan sha’anin ruwa da raya karkara, yace akwai bukatar yin la’akari da wadannan sassan wajen wannan sabon nazarin.
A nasa bayanin, babban sakataren hukumar raya kogunan Jama’are da Hadejia Dr. Ado Kalid, ya bayyana cewa wannan damuwar da ake fuskanta na da nasaba da kafewar tafkin Chadi.
Facebook Forum