Muryar Amurka ta yi tattaki zuwa wasu sansanonin domin tabbatar da sahihancin labarin duk da cewa ita gwamnatin jihar ta musanta batun.
Shugaban hukumar samarda agajin gaggawa na jihar Alhaji Grema Sheraf yace batun ba gaskiya ba ne. Maimakon hakan ma gwamnatin jihar na cigaba da ciyar dasu kamar yadda aka saba.
An sha yin jita-jita cewa gwamnatin jihar zata kwashe 'yan gudun hijiran tunda an kammala zabuka domin wai gwamnati bazata cigaba da daukan nauyin ciyar dasu ba ganin yadda ta rage kayan abincin da take basu. Da suna samarda abinci sau uku rana guda amma yanzu ya koma sau biyu kawai.
Wasu 'yan gudun hijiran da aka zanta dasu akan lamarin sun tofa albarkacin bakinsu. Sun tabbatar suna samun abinci da ruwa.Sun ce ba'a yi masu batun cewa za'a kwashesu alatilas a mayar dasu gidajensu ba. Yawancinsu sun yi kukan rashin sutura duk da cewa sun yi fiye da shekara daya a sansanonin. Sai kuma bakin talauci da suke fama dashi. Hatta sabulun wanka ko na wanki basu dashi.
Akwai 'yan gudun hijira fiye da dubu dari daya da ashirin a sansanoni tara.
Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.