An shiga sati na uku ke nan, da wata kotu a birnin Ikko ta yankewa Major Hamza Al-Mustapha hukuncin kisa.
To amma kuma tun daga lokacin kawo yanzu, lauyoyin Al-Mustapha suna safa da marwa domin neman samun wannan hukunci ko shari'a a rubuce, wanda zasu yi amfani dashi wajen daukaka kara.
Wannan al'amari yasa yan uwan Al Mustapha ke cewa kila jita jitan da suke ji cewa za'a sawa Al Mustapha guba a cikin abinci ya zame gaskiya.
A wata hira da sashen Hausa, kanin Al-Mustapha, Hadi Al-Mustapha ya shedawa wakilin sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa cewa suna jin jita jitan cewa za'a yi kokarin asawa Al-Mustapha guba a cikin abinci domin a tabbata cewa ya mutu.
Hadi yace su dai gwamnati ba zasu saki Al-Mustapha da rai ba, zassu yi iyakacin kokarin su tabbata sun kashe shi.. Amma kuma yace sun bar komai hannun Allah, domin kuwa shekaru goma sha hudu ke nan ake yi musu rashin adalci.
Da wakilin sashen Hausa ya tuntunbi lauyan Al-Mustapha, sai ya ce dashi ya zuwa ranar ashirin da uku ga wannan wata na fabrairu da nake magana da kai, ba'a basu hukuncin a rubuce ba. Yace an gaya musu cewa har yanzu ba'a gama bugawa akan keken rubuta ba.
Lauyan Al-Mustapha yana bukatar wannan hukunci a rubuce domin ya daukaka kara. Ya kuma ce zai ci gaba da neman an bashi wannan hukunci a rubuce, domin ya daukaka kara.