Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kara Nuna Damuwa Game Da Masu Kishin Islama A Arewacin Mali


Mayakan Kungiyar Ansar Dine na kasar Mali a hamadar bayan garin Timbuktu, ranar 24 Afrilu, 2012.
Mayakan Kungiyar Ansar Dine na kasar Mali a hamadar bayan garin Timbuktu, ranar 24 Afrilu, 2012.

Wakilan Majalisar tsaro da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka sun yi kashedin cewa masu kishin Islama, ciki har da al-Qa’ida, sun kuduri aniyar kafa wata sabuwar tunga ta ayyukansu a yankin

Ana kara nuna damuwar cewa masu kishin Islama a yankin arewacin kasar Mali zasu iya haddasa rashin kwanciyar hankali a fadin yankin Afirka ta Yamma baki daya.

Jiya asabar wakilan Majalisar tsaro da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka dake taro a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, suka yi kashedin cewa masu kishin Islama, ciki har da al-Qa’ida, sun kuduri aniyar kafa wata sabuwar tunga ta ayyukansu a yankin.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka, KTA, Jean Ping, ya bayyana wannan lamarin a zaman daya daga cikin fitinu mafiya muni da suka taba addabar nahiyar Afirka. Shi ma Kwamishinan ayyukan tsaro da zaman lafiya na KTA, Ramtane Lamamra, ya ce kara karfin da kungiyoyin ‘yan ta’adda da na masu aikata laifuffuka suka yi a yankin yana barazana mummuna ga zaman lafiyar duniya.

Masu kishin Islama sun fake da tawayen da Abzinawa ‘yan aware suka kaddamar a makekiyar hamadar arewacin kasar suka kwace wannan yanki. Kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi sun lalata kaburburan shaihunan malamai Musulmi sufaye bisa ikirarin cewa ziyartarsu ridda ce.

KTA tana aiki tare da kungiyar tarayyar tattalin arzikin Afirka ta yamma, ECOWAS domin tallafawa gwamnatin riko ta Mali wadda aka kafa a bayan juyin mulkin 22 ga watan Maris, da kuma tattauna zabin da ake da shi na takalar masu kishin addinin.

Har ila yau shugabannin Afirka suna neman goyon bayan Kwamitin Sulhun MDD domin daukar matakan soja a kasar Mali da nufin kawo karshen tawayen arewacin kasar da sake hada kasar dake yankin Sahel.

XS
SM
MD
LG