Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gumurzu Kan Wasu Tasoshin Jigilar Mai A Libiya.


Wata tankar mai a gabar daya daga cikin tasoshin jigilar mai na Libiya.
Wata tankar mai a gabar daya daga cikin tasoshin jigilar mai na Libiya.

Yinkurin kwace wasu tasoshin jigilar mai masu muhimmanci a Libiya ya haddasa kazamin yaki.

A Libiya, an cigaba da yaki jiya Asabar na kokarin kwace tasoshin jigilar mai da ke wajejen birnin Benghazi. Sojojin Kishin Kasar Libiya, ko LNA a takaice, wadanda ke gabashin kasar, sun sallamar da iko da akalla wata babbar tashar jigilar mai wadda su ka kwace bara.

Janyewar ta LNA, ta biyo bayan farmakin da wani bangare da ya balle mai suna Dakarun Kare Benghazi, ko BDB a takaice ya kai.

Ahmed al-Mismari, mai magana da yawun LNA, ya gaya ma kafar labaran Reuters cewa kungiyar ta LNA ta maida martani kan harin da aka kai kan tasoshin mai din ne da kaddamar da hare-haren jiragen sama a Ras Lanuf, Es Sidra, Ben Jawad da Harawa.

Yinkurin na kwace tasoshin jigilar man Libiya, ya dada janyo fargabar yiwuwar a fuskanci karin tashe-tashen hankula a yankin.

Bayan da LNA ta kwace tasoshin jigilar mai hudu a watan Satumba, sai adadin man da Libiya ke samarwa ya karu sosai, wanda ya zama wani kalubale ga hukumar da ke samun goyon bayan MDD, wadda ke da fada a Tripoli.

XS
SM
MD
LG