Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karancin Abinci A Nijar Sakamakon Takunkumin ECOWAS


Wani rumbun ajiyar kayan abinci
Wani rumbun ajiyar kayan abinci

Duk da matakin rage kudin harajin kayayyaki da gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yi wa 'yan kasuwa, har yanzu ana fuskantar karancin cimaka da sauran kayayakin bukatun yau da kullum a wasu sassan kasar.

AGADEZ, NIGER - A kokarin magance tasirin takunkuman kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta kakabawa wa Nijar bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan yuli wanda ya haifar da karancin cimaka da kuma tsadar kayayyakin masarufi, gwamnatin mulkin sojin Nijar ta rage kashi 25 cikin 100 na kudin shigo da kayan abinci ga yan kasuwa.

To sai dai duk da wannan matakin, har yanzu ana fuskantar karancin abinci da ma sauran kayayyakin bukatun yau da kullun musanman shinkafa, da ke matsayin jigon abincin da mafi yawan al’ummar kasar ke amfani da ita.

Al’ummar kasar na kokawa kan abin da suka kira halin kunci sakamakon tsadar kayan abinci, inda ake sayar da buhun shinkafa akan farashin 15,000 zuwa sama, a cewar wasu magaidanta a birnin Agadas.

To saidai kungiyoyin da ke yaki da tsadar rayuwa a Nijar sun yi kira ga gwamnatin mulkin sojin kasar da su sanya ido sosai akan ‘yan kasuwa don ganin cewa ba’a kuntatawa talakawa ba.

Gwamnatin mulkin sojin dai ta kafa wani kwamitin da zai rika sanya ido kan ‘yan kasuwa, wanda burinsa shine duba irin yadda ake sayar da kayan abinci a kasuwannanin kasar.

To saidai ‘yan kasuwar na ganin dokar haramcin fitar da shinkafa da kasar Indiya ta yi, shi ne ya shafi wasu kasashe ciki har da Nijar.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Ana Fama Da Rashin Abinci A Nijar Sakamakon Takunkumi ECOWAS Da CEDEAO.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG