Wadansu ‘yan majalisar dokokin kasar Zimbabwe guda hudu sun yi kaciya a yunkurin wayar da kan al’umma dangane da illar cutar kanjamau.
‘Yan majalisar wadanda suka fito daga manyan jam’iyun siyasar kasar dake adawa da juna, Jam’iyar shugaba Robert Mugabe, ZANU-PF da kuma ta Firai Minista Morgan Tsvangirai, MDC, sun dauki matakin hadin guiwar a yunkurin shawo kan cutar.
Binciken Hukumar lafiya ta duniya na nuni da cewa, yiwa maza kaciya yana rage hadarin kamuwa da kwayar cutar HIV da kasshi 60%.
Kasar Zimbabwe tana amfani da wannan hanyar wajen yaki da cutar kanjamau da tayi kamari a kasar.
A shekarar alib da dari tara da casa’in kasar Zimbabwe ce tafi kowacce kasa a duniya yawan masu fama da cutar kanjamau, yayinda aka sami kimanin kashi 13.7% na mutanen da suka balaga a kasar dauke da kwayar cutar a 2009.