Idan gwamnatin tarayya na ganin rike kudin jihar zai hanata yiwa jama'a aiki to a rufe babban bankin kasar kada a ba kowa nera-inji gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar.
Gwamnan yayi furucin ne a garin Gumi cikin jihar ta Zamfara inda ya kaddamar da kemfen din neman a sake zabarsa a matsayin gwamnan jihar zagaye na biyu.
Ya zargi gwamnatin Najeriya da kin biyan jihar kudadenta bisa ga ra'ayin banbancin siyasa da kuma kulla makarkashiyar kawo cikas ga tafiyar da ayyukan gwamnatin Zamfarar.
Gwamnan yace sun yi ayyuka na sama da nera biliyan talatin. Ya shaidawa shugaban kasa wanda yayi masa alkawarin biyan kudin. Wai har ya sa a biya saidai daga baya ya gayawa gwamnan cewa babu kudi. Shugaban yace zai sa bankuna su lamuntawa jihar idan ya biya sai a ba bankuna kudinsu.
To saidai inji gwamnan 'yan PDP na jihar Zamfara sun kawo cikas. Sun fadawa gwamnatin tarayya cewa ita jiha zata yi anfani da kudin ne ta wata hanya daban. Sun ce siyasa za'a yi da kudin.
Amma wani jigo a jam'iyyar PDP kuma tsohon dan majalisar wakilai Sani Muhammad Anka yace gwamnatin tarayya ta fada tun farko cewa idan jihar tayi aikin da inganci kamar yadda gwamnatin tarayya ta tanada to zasu biya. Bayan an gama aikin gwamnan ya gayyato dan takarar shugaban kasa na APC Janaral Buhari ya kaddamar da aikin wanda shi ma yace aikin yayi tsada.
Anka yace babu wanda ya hana a biya jihar amma gwamnan ne ya sabawa alkawarin da aka yi dashi.
Ga karin bayani.