Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga Zangar Kin Jinin Shugabancin Adams Ashimole A Zamfara


Zanga-zangar adawa da shugabancin Adams Ashimole
Zanga-zangar adawa da shugabancin Adams Ashimole

Dubun-dubatar ‘yan jam’iyyar APC jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin Shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole.

Zanga-zangar ta lumana ta kumshi dukkan shugabannin jam’iyyar na matakin kananan hukumomi da mazabu, da ma sauran ‘yan jam’iyyar daga sassan jihar daban-daban.

Masu zanga zangar sun soma da zagaya titunan Gusau babban birnin jihar, kafin su karkare a shelkwatar jam’iyyar, inda suka gabatar da korafinsu, ta bakin shugaban dandalin shugabannin ja’iyyar na kananan hukumomi, kuma shugaban jam’iyyar na karamar hukumar mulkin Maru, Aminu Abdullahi Gama-Giwa.

Zanga-zangar ta kuma hada har da wasu mukarraban gwamnati kamar kwamishinoni da masu bada shawara na musamman na gwamnan jihar.

Sai dai mataimakin shugaban majalisar karamar hukumar mulki ta Zurmi, Abubakar Daura yace ba dukkan ‘yan jam’iyyar ta APC a jihar ne suka yi zanga-zangar ba.

Wannan lamarin dai ya biyo bayan takaddamar zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APC wanda bai yiwu ba, duk da yake bangaren gwamnatin jihar sun ce sun gudanar da zaben, to amma kuma uwar jam’iyyar a karkashin Adams Oshimhole, tayi watsi da shi.

Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna

Zanga zangar adawa da shugabancin Oshimole-2:57"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG