Mahalartan taron sun fito ne daga ciki da wajen Najeriya.
Dr Yakubu Magaji Azare shugaban kwamitin shirya taron ya bayyana makasudin taron.
Yace shekaru da dama ana gudanar da fasara a kafofin yada labarai da kotunan shari'a da majalisun dokoki da ma hukumomi masu zaman kansu domin isar da wani sako. Yace an fahimci cewa ana yawan samun kurakurai ko kuma rashin daidaito wajen yadda ake gabatar da fasare fasare.
A wasu lokutan ma akan samu wadansu da basu cancanta a ce sun shiga cikin yin fasara ba. Amma suna yi mata kutse suna shiganta da ka.
Masana da shehunnan malamai su ne suka gabatar da makaloli kan dabarun aikin fasara da tafinta. Batun sabuwar figa ko fasahar fasara ta kafar internet da ake kira google translate ita ce makalar Farfasa Salisu Yakasai na sashen koyarda harsunan Najeriya a jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto.
Farfasa Yakasai yace yanzu likkafar Hausa ta yi gaba domin ta samu shiga cikin rukunin tsari na fasara. Da an buga za'a samu fasara na kalmomi har da wasu bayanai ko juloli. Wannan sabuwar fasaha ta zauna daram ko ana so ko ba'a so.
Wata ba'amarikiya da ke nazari akan harshen Hausa da ta halarci taron tace tana da sha'awar fasara daga Hausa zuwa Turanci sabilin kasancewarta ke nan a wurin taron. Idan akwai kungiyar fasara zata iya bata fasararta a duba mata.
Malam Ado Ahmed Gidan Dabino wani shahararren marubucin littafan Hausa yace fasare fasaren baya tun daga Abubakar Iman yanzu sun banbanta. Yakamata a kawo daidaito da abun da ya faru jiya da yau.
Ga karin bayani.