Yayin da malamai ke ta rufe tafsiran watan Ramadan mai karewa, sun yi ta jawabai na gargadi game da illolin almundahana da dukiyar jama’a da kuma ta’addanci. Malaman sun nesanta Musulunci da ta’addanci, tare da cewa duk wanda ya shiga aikin ta’addanci to ya saba ma karantarwar Alkur’ani Mai Tsarki da Hadisai. Haka kuma duk wanda ya yi amfani da matsayinsa a gwamnati ya cuci jama’a to zai gane kurensa ranar hisabi.
Mai tafsiri a Masallacin Jumma’a na Maitama Abuja, Sheikh Suraj Alhaji Sabo Keffi ya shawarci ma’aikatan gwamnati da su kauce ma cin dukiyar jama’a saboda bala’in da zai biyo baya musamman ranar kiyama. Sheikh Keffi ya kuma ce akwai ayoyin Alkur’ani da dama inda Allah ya bayyana cewa ta’addanci ya yi hannun riga da addinin Musulunci. Bayan da Sheikh din ya kawo aya sai ya kara da cewa, “Babu yadda Musulunci zai ce ku je ku fada masallaci ku kashe mutane ku kashe kanku; babu inda Musulunci ya ce: jeka ka shiga coci ka kashe mutane ka kashe kanka; babu inda Musulunci ke cewa ku je wurin wasu mutane su yi Musuunci dole ,.” Sheikh Keffi ya kara da jan aya ta 2:256 da ke cewa, “La ikraha fiddini,” ma’ana, “babu tilastawa ga addini.”
A Masallacin Usman bin Affan da ke Wuse ii kuwa Sheikh Husaini Zakariya ya rufe tafsirin ne da kira ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya kula da cewa mutane na fama da kuncin rayuwa. To amma kuma ya yaba da saukin da aka samu game da matsalar Boko Haram. To ama Shiekh Zakariya y ace sun kai ziyara sansanonin ‘yan gudun hijira kuma sun ga abubuwan juyayi da ke bukatar Shugaban kasa ya sani.
Daga Abuja ga wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton: