Shaikh Abubakar Jibril babban limamin masallacin Juma'a na harabar Jami'ar Bayero tsohuwa ya jagoranci sallar masallacin Idi na jami'ar.
Sallar Idin a Kano an gudanar da ita ne cikin masallatan Juma'a saboda ruwan sama da ya dinga zuba tun sallar asubahi ta yau
Dr. Muhammad Sani Ayagi yayi bayanin hudubar da limamin ya bayar a masallacin Jami'ar Bayeron. Ya fadi mahimmancin ranar a musulunci da girmanta da darajarta kana ya jawo hankulan jama'a da su shagala da abubuwa nagari.
Limamin ya bayyana yadda Allah ke son layya ya kuma fadi sharrudanta. Layya ana yinta ne domin Allah kana ya jawo hankalin jama'a da basu da halin yanka ragon layya su mayarda lamuransu ga Allah, kada su sa kansu cikin takura saboda Manzon Allah ya yi masu layya..
Duk da ruwan jama'a sun halaraci sallar sallah.
An kira jama'a da su kaunaci juna tare da kasar da kuma yiwa kasar addu'a.
Shi ma ajawabinsa Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya kira jama'a da su guji dabi'un dake sa tattalin arzikin kasar ya kara tabarbarewa.
Ga rahoton Mahmud Kwari da karin bayani.