Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi jana'izar wadanda suka rasa rayukansu a gobarar tankar dakon mai

gobara tana ci
gobara tana ci

A kalla mutane 100 ne suka mutu jiya Alhamis a wani hadarin mota da ya hada da wata motar dakon mai a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a Najeriya.

A kalla mutane 100 ne suka mutu jiya Alhamis a wani hadarin mota da ya hada da wata motar dakon mai a yankin Niger Delta mai arzikin man fetir a Najeriya.

Hukumomi sun ce mutane da suka yi ruga domin su kwashi man da yake kwarara sun rasa rayukansu a gobarar da ta tashi bayan faduwar motar.

Wakilin Sashen Hausa dake yankin Niger Delta Lamido Abubakar wanda yaje inda hadarin ya afku ya ruwaito cewa, wadansu kimanin mutane arba’in sun ji raunuka. Ya zuwa daren jiya dai hukumomi sun bayyana cewa an yiwa sama da mutane 85 jana’izar bai daya.

XS
SM
MD
LG