Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Mutanen da Aka Kashe a Jihar Zamfara


Mutanen da aka kasha a jihar Zamfara, lokacin da ake yi musu jana'iza.
Mutanen da aka kasha a jihar Zamfara, lokacin da ake yi musu jana'iza.

Mutanen da aka kashe a wani hari da aka kai a kusa da garin Dansadau, dake jihar Zamfara, an yi masu jana'iza na bai daya.

Mutane fiye da dari da wasu 'yan bindiga akan babura suka kashe a garin Unguwar Galadima, ta gundumar Dansadau dake karamar hukumar Maru, jihar Zamfara, sun samu jana'iza ta bai daya.

Gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, da mataimakin sifeton janaral na 'yan sanda, Mamman Sule sun samu halartar jana'izar.

Farmakin da yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dari da ashirin ya faru ne da yammacin Asabar, lokacin da manoma da kungiyoyin 'yan banga daga jihohin Zamfara da Kebbi da Katsina da Kaduna suke wani babban taro a garin na Unguwar Galadima.

Suna taron ne domin samun mafita daga hare-haren da ake kaiwa a yankunasu.

Mutanen da suka abka masu sun zone akan babura, dauke da bindigogi da adduna. Sun harbe wasu, kana kuma sun sassare wasu.

Wani Abdullahi Useini na Unguwar Galadima yace "talakawa ne suka hadu domin kwato 'yancin kansu saboda abubuwan da ake yi masu sun ishesu. Suna cikin taro Allah Ya kawosu. Da suna zaton mutanen taron suka zo, sai da suka ga suna harban mutane, suna murde wa wasu wuya wasu kuma sun fasa kawunansu." A lissafin Abdullahi Useini, an samu rasuwar mutane 155. Akwai wasu da ba'a gansu ba, amma za'a cigaba da nemansu.

A jawabin da gwamnan jihar, Abdulazaiz Yari yayi a wurin jana'izar, ya dora alhakin abunda ya faru akan taron, domin an yi shi ne ba akan ka'ida ba. Yace "idan za'a shirya irin taron dole a nemi izini. Wanda ya shirya taron yana da wani dalili. Gwamnati da jami'an tsaro zasu yi binciken kwakwaf a gano wadanda suka shirya taron har ya kaiga asarar rayuka. Duk wanda aka samu da hannu ciki za'a hukuntasu komai girmansu ko martabarsu." Yace a matsayinsa na gwamnan jihar, babu abun da yasa gaba, illa kare rayukan 'yan jihar da dukiyoyinsu da tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

A 'yan shekarun nan, jihar ta sha fama da hare-hare musamman a yankin gundumar Dansadau, lamarin da yayi sanadiyyar rayukan daruruwan jama'a. Amma wannan harin na ranar Asabar, shi ne mafi muni, wanda ya rutsa da rayuka fiye da dari da hamsin.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG