Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Mutanen Da Suka Mutu A Harin Cocin Owo


Lokacin jana'izar mutanen da aka kashe a harin Owo
Lokacin jana'izar mutanen da aka kashe a harin Owo

A ranar 5 ga watan Yuni, ‘yan bindiga suka kai hari Cocin Saint Francis Catholic Church da ke garin Owo a kudu maso yammacin Najeriya inda suka datse kofar mujami’ar suka bude wuta.

Cikin yanayi na juyayi da ya kai ga zubar da hawaye daga mutane da dama, an gudanar da taron addu’o’in jana’izar mutanen da wasu ‘yan bindiga suka kashe a wata Coci da ke garin Owo a jihar Ondo.

A ranar 5 ga watan Yuni, ‘yan bindigar suka kai hari Cocin Saint Francis Catholic Church da ke garin na Owo a kudu maso yammacin Najeriya inda suka datse kofar Mujami’ar suka bude wuta.

Akalla mutum kusan 40 suka mutu.

Jana’izar ta samu halartar gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu da mai dakinsa Chief Betty Anyanwu wacce aka yi a Mydas Resort Hotel da ke garin na Owo kamar yadda wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar dauke da sa hannun Sakataren yada labarai Richard Olatunde ta fada.

Gwamna Akeredolu, wanda ya zubar da hawaye yayin taron addu’o’in ya nuna gazawar gwammati wajen kare jama’a daga wannan aika-aika.

Gwamna Akeredolu, hagu, da matarsa Betty suna kuka a lokaci jana'izar
Gwamna Akeredolu, hagu, da matarsa Betty suna kuka a lokaci jana'izar

“Mun gaza kare wadannan mutane, ba wai don ba mu gwada yin hakan ba, sai dai don wadanda suka aikata wannan danyen aiki suna da goyon baya, ba za su taba yin nasara akanmu ba.” Akeredolu ya ce.

Akeredolu ya kara da cewa, akwai bukatar mahukunta su yi wani, yana mai cewa lokaci ya yi da za a yi garambawul ga fannin tsaron Najeriya.

Yayin nasa jawabin, Limamin Mabiya darikar Katolika a jihar Ondo, Dr. Jude Arogundade, ya bayyana cewa Gwamna Akeredolu bai gaza wajen kare al’umar jihar ba.

Akalla mutum 22 aka yi wa jana’iza a ranar ta Juma’a duk da cewa mutum 41 aka tabbatar da sun mutu a harin.

“Mamata 22 ne a wannan dakin taron. An riga an binne wasu kalilan, saboda ‘yan uwansu sun ce ba za su iya jira har zuwa yau ba, amma a kididdiga ta karshe da muka yi, mutum 40 aka kashe.” In ji Akeredolu.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG