Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Gangami Akan Illar Muzgunawa Mata da Yara A Birnin Legas


Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode
Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode

Saboda da yadda cin zarafin mata da yara ke karuwa a Legas da kewaye ya sa wasu dake fafutikar kare hakin dan Adama suka shirya gangamin fadakar da kawunan mutane aka illar dake tattare da wannan mugun hali.

Wata kungiya mai fafautikar kare hakkin bil Adama musamman mata da yara ita ce ta shirya gangamin fadakar da al'umma akan illar cin zarafin mata da yanzu yake son ya zama tamkar ruwan dare gama gari.

Shugaban kungiyar Dr Joe Odumakin ya yi karin bayani game da gangamin. Yace muzgunawa mata na karuwa a kasar. Kawo yanzu mata ukku sun rasa rayukansu saboda ukubar da suka sha walau daga mazajensu ko wasu daban. Saboda haka akwai bukatar wayar da kawunan al'umma tare da bukatan gwamnati ta dauki matakai domin kare mata da yara.

Alkalumma sun nuna cewa kashi biyu cikin ukku na mutanen da ake muzgunawa mata ne. Dalili ke nan da wani namiji yace akwai bukatar wayar da mutane, musamman maza, akan illar muzgunawa mata da yara.

Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG