Sama da jami'an tsaron 583 ne da suka fito daga kasashen Africa irinsu Kamaru, Mali, Ivory Coast, Congo Guinee dakuma jamhuriyar Africa ta tsakiya suka samu horon dubarun yaki na tsawan watanni goma (10) a makarantar horar da sojoji ta ENSOA dake Agadas.
Wannan horon na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron kasar Nijar ke yaki da ta'addanci. Ministan Tsaron Kasar Nijar Alkasum Indatu shi ne ya jagoranci bikin. Ya ce wannan abun farin ciki ne na yaye da aka yi na jami'an kuma za mu rarraba su zuwa fagen daga. Ya kara da jan hanakli jami'an da suka sami horon da su dage wajen samar wa kasar ingataccen tsaro.
Masu sharhi kan al'Amurran tsaro na ganin wannan a matsayin hanyar da za a magance tsaro kuma ta kara adadin sojojin da kasar Nijar ke dasu da kuma basu wadatattun kayan aiki kamar yadda Ibrahim Manzo Jallo, mai sharhi kan al'amuran tsaro a Agadas ya bayyana.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: