An yi wannan biki na wannan shekara a Yola fadar jihar Adamawa, inda cibiyar kawo fahimtar juna tsakanin mabiya addinin Islama da kirista ta shirya wata bita tareda hadin guiwar Jam'ar Amurka ta Najeriya a Yola.Taron ya hada da shugabbanin wadannan addinia da kungiyoyin farar hula masu ayyukan ci gaba ne suka halarta.
Da yake magana da wakilin Sashen Hausa, kan muhimmancin wannan rana, shugaban cibiyar mai kula da shiyyar jihohi da suke arewa maso gabas, Mallam Abdullahi Damare, yace makasudin shirya taron shine gano hanyoyin kawo karshen yawan zubda jini yau anan gobe a can, jibi a can, d a hasarar dukiya masu yawa. Yace akwai bukatar jama'a suk kara sanin cewa "zaman lafiya yafi zama dan sarki"..
Daya daga cikin mahalarta taron, malama Cahity Garba, tace tun 1982 Majalisar Dinkin Duniya ta fara shirya wannan taro, kuma yana da kyau saboda idan babu zaman lafiya, babu wani abund a za a iya tabukawa.