An yankewa shahararren mawakin Amurka R. Kelly hukuncin zaman gidan yari har tsawon shekara 30 saboda ya yi amfani da daukarar da ya samu wajen gudanar da ayyukan lalata da kanana yara, a cewar AP.
Mai Shari’a Ann Donnelly ce ta ayyana hukuncin a wata kotu da ke unguwar Brooklyn a birnin New York a ranar Laraba.
A shekarar da ta gabata kotu ta sami R.Kelly da laifi a shari’ar wacce masu zarginsa suka fara tunanin an ki sauraren kokensu saboda su bakaken fata ne.
An samu R.Kelly da laifin yaudarar matasan mata da mata yara kanana wadanda suka ce ya ci zarafinsu ta hanyoyi da dama da suka hada har da lalata.
Tun a shekarun 1990 aka fara zargin R.Kelly mai shekaru 55 da wadannan laifuka amma lamarin bai yi tasiri akansa ba saboda shahararsa.
Mai Shari’a Donnelly ta ce dokar kasa ta ba da iznin yanke hukuncin da ya kai daurin rai da rai a irin wannan shari’a.
Lauyoyin R.Kelly sun nemi da a yanke masa shekaru 10 ko kasa da haka. Tun a shekarar 2019 ake tsare da R. Kelly ba tare da an ba da belinsa ba.
Har yanzu yana fuskantar wata shari’a kan zargin ayyukan bidiyon lalata da kananan yara inda ake sa ran za a fara shari’ar a ranar 15 ga watan Agusta.
R.Kelly ya yi fitattun wakoki irinsu, “I Believe I Can Fly,” da “Storm Is Over” wadanda suna daga cikin wakokin da suka sa ya samu daukaka.