Wani tsohon dan wasan kwallon kafa na kasa-da kasa mai suna, Etim Esin, ya yaba da nada tsofaffin shahararrun 'yan wasan Super Eagle, Jay-Jay Okocha, Kanu Nwankwo da kuma Tijjani Babangida, inda ya ke cewa za su karfafwa tawagar ta Super Eagle gwiwa a gasar cin kofin Nahiyar Afrika da za a yi mai zuwa a kasar Masar.
Kwanan ne hukumar kula da kwalon kafar Najeriya ta nada 'yan wasan mutum uku da suka yi fice a tawagar kwallon kafar kasar, yayin da kungiyar Super Eagle ta ke shirye-shirye don zuwa neman ta lashe gasar cin kofin Afrika karo na hudu.
Shahararrun 'yan wasan da aka daurawa alhakin su kula da duk wasu wasanni da kungiyar Super Eagle za ta buga da abokan hamayyarta da zai kaita zuwa matakin wasan karshe a gasar da za a yi a Masar, kuma za su kasance a karkashi mai horar da kungiyar, Gernot Rohr, sannan za su ci gaba da gudanar da aikin su a lokacin gasar a Masar.
Sannan kuma ya bayyan cewa matakin nadin Jay-Jay Okcha, Kanu Nkwankwo da kuma Tijjani Babangida, an saka kwarya a gurbinta.
Facebook Forum