Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Umurci Dubban Mutane su Tashi


Kauyan Pakistan ne ke ratsa ruwan ambaliya a Baseera, Pakistan.
Kauyan Pakistan ne ke ratsa ruwan ambaliya a Baseera, Pakistan.

Jami’an gwamnatin Pakistan sun Umurci Dubban Mutane su Gudu, a Sa’ilinda Ambaliyar Ruwa ke Dada Munana.

Jami’an gwamnatin Pakistan sun umurci mutane masu yawan kimanin 400,000 na wasu garuruwan kudancin kasar uku da wata sabuwar ambaliyar ruwa ke wa barazana da su gudu daga wuraren.

Yau Alhamis ce dai hukumomin su ka yi gargadin bayan da kogin Indus da ke lardin Sindh ya cika mal. Jami’an gwamnati su ka ce mazauna Sujawal, da Mir Pur Batoro da kuma Daro da fuskantar barazana. Hukumomi kuma a Gundumar Thatta na ta kokarin samar da hanyoyin kwararar ruwa, sannan kuma an tura sojoji su kwashe jama’a.

A sa’ilinda ambaliyar ta yi sauki a wasu sassan na Pakistan, kwararru su ka ce cikar da tekun Arabiya ta yi na barazanar haifar da wata sabuwar ambaliyar ruwan a Sindh.

Ruwa kamar da bakin kwarya ne ya haddasa ambaliyar da aka soma tun kusan wata guda ta ya wuce, wadda ta hallaka kimanin mutane 1,600 ta kuma shafi mutane miliyan 20.

Jami’an gwamnatin Pakistan da na Amurka sun yi gargadin cewa mayakan sa kai na masu tsattsauran ra’ayin Musulunci na iya amfani da damar da ambaliyar ta haifar. Yau Alhamis, wani jami’in gwamnatin Amurka wanda bai son a ambaci sunansa ya gaya wa kafafen yada labaran BBC da AFP cewa mai yiwuwa kungiyar Taliban a Pakistan ta auna ma’aikatan agaji ‘yan kasashen waje da ke aikin ceton.

Wani kakakin kungiyar Taliban ya kalubalanci manufar Amurka da ta ke taimakawa ya kuma gaya wa kafafen yada labarai cewa kungiyar ta Taliban ba za ta amince da gudunmowar Amurka ba.

Kakakin sashin agaji na Majalisar Dinkin Duniya Maurizio Giuliano ya bayyana duk wani yiwuwan hari kan masu taimakawa na kasa da kasa da cewa dacin rai ne.

XS
SM
MD
LG