Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tura Jiragen Yaki Jahar Filato


Wani jirgin saman Najeriya
Wani jirgin saman Najeriya

Babbar magana, wai dan sanda ya ga gawar soja. Wannan magana na nemar tabbata a jahar Filato, inda aka tura sojojin sama da ku,a jiragen yaki saboda ganin yadda rigimar da ake yi, ga dukkan alamu, ta fi karfin 'yansanda.

Ganin yadda aka yi ta zubar da jini a rikicin jahar Filato, wanda ya ki ci ya ki cinyewa, Rundunar Sojin Saman Najeriya ta tura jiragen yaki da sojoji da kuma wasu kayan yaki don dakile wannan rigimar, wadda ake ganin ta fi karfin ‘yan sanda.

Game da takaddamar da ake yi kan ko ya dace a tura sojoji su yi aikin da a bisa al’ada na ‘yansanda ne, Babban Hafsan Hafsohsin Rundunar Sojin Saman Najeriya Air Mashar Sadik Abubakar Yabani ya ce akwai ka’idar kai sojoji inda ya kamata ace ‘yansanda ne ke kwantar da hankali. Ya ce an bi wannan ka’idar kafin a yanke shawarar tura sojojin. Haka zalika, wani lauyan kundin tsarin mulkin kasa kuma dan rajin kare hakkin dan adam, Barrister Yakubu Bawa ya ce idan ta kama ana iya tura soja a wuri mai fama da dadden rikicin da aka kasa shawo kansa.

Ga wakilinmu a Abuja, Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG