Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tantance Mayakan Boko Haram 57 Da suka Mika Makamai


BORNO: 2Lt. Adeosun kwamandan dakarun dake yaki da 'yan Boko Haram
BORNO: 2Lt. Adeosun kwamandan dakarun dake yaki da 'yan Boko Haram

Rundunar tsaron Najeriya ta Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri ta nunawa manema labarai wadansu mutane su hamsin da bakwai da tace ‘yan kungiyar Boko Haram ne da suka watsar da makamansu, suka kuma mika kansu da kansu ga jami’an tsaro.

Rundunar tace mutane saba’in ne yanzu haka suka ajiye makamansu, wadansu kuma suka mika kansu ga jami’an tsaron, Sai dai wadanda aka riga aka tantance yanzu su hamsin da bakwai ne, amma sauran suma suna nan tafe.

Kwamandan rundunar sojan na operation lafiya dole, Majo janar Ibrahim Attahiru, yace mayakan sun mika kansu ne a wadansu kauyuka biyu dake karamar hukumar Gwoza, ya kuma bayyana cewa, kimanin ‘yan kungiyar Boko Haram dari bakwai sun bayyana niyarsu ta yin saranda, da ajiye makamai, amma kawo yanzu mutane hamsin da bakwai ne kawai suka ajiye makamai.

Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana da wani shiri ga mutanen da suka mika kansu da kansu da ake kira “Operation safe corridor” domin sake tsugunar da su, da koya masu sana’oi yadda zasu iya rayuwa cikin al’umma ba tare da tsangwama ba.

A cikin hira da manema labarai, mutanen da suka mika makamansu, sun bayyana cewa, sun tsaida shawarar ficewa daga kungiyar ne domin sun gane cewa, dabi’unsu ba kan hanya suke ba.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana daga Maiguguri.

Yan boko Haram 57 sun yi saranda 3'35
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG