WASHINGTON, DC —
Shaidun gani da ido sunce a kalla mutane 100 ne suka rasa rayukansu a rigingimun kabilancin da suka barke a karshen wannan mako a garin Wukari, jahar Taraba. Yayin da hankula ke neman kwantawa, yanzu haka dubban jama’a na cikin wani mawuyacin hali na rashin matsuguni da kuma abinci, inda ake tsoron barkewar cututtuka. A rahoton da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya aiko wani dan garin yayi bayani kamar haka:
An Tafka Asarar Rayuka da ta Dukiyoyi a Rikicin Wukari
![Sojojin kwantar da tarzoma na kokarin kashe wutar rikici a Wukari, jahar Taraba.](https://gdb.voanews.com/0b27b144-83b5-46ba-ba84-13c7212a3e2f_w250_r1_s.jpg)
Baicin kona gidaje,akwai kuma matsalar rashin abinci inji wani dan garin da yayi kira a kafa mu su sansanonin zama