Dubban wakilan kasashen duniya daban-daban na halartar babban taron kasa da kasa da aka soma a nan Washington akan yaki da cutar kanjamau mai karya garkuwar jii ta AIDS/SIDA, wanda yau aka shiga rana ta ukku da soma shi.
A jawabin da tayi jiya awurin taron, Sakatariyar Ma'aikatar harkokin wajern Amurka Hillary Clinton tace Amurka ta daura damarar ganin cewa an sani al’ummar da bata da wannan cuta.
Saboda haka ne tace a shirye Amurka take ta tanadi mankudan kudaden da za’a yi anfani da su a kasashen Afrika da sauran kasashen wajen yakar wannan cutar, musamman don hana iyaye mata baiwa ‘yayansu jarirai wannan mummunar cutar.
Ta kuma yaba da wasu sababbin matakan yin kaciya da aka fito da su a kasashen Afrika dake hana wanzuwar daukar kwayar cutar ta HIV/AIDS a cikin hanzari.