Dutsen Azurfa rawaya da ba safai ba ake samunsa ba, da aka gano a Afirka ta kudu, wadda aka hakikance shine mafi girma a Duniya, an sayar da shi kan kudi dala milyan 12 da dubu dari uku.
Kamfanin gwanjo da ake kira Sotheby dake Geneva ne ya sayar da zinarin mai darajar karat-110, jiya talata aka sayar da dutsen.Ba a san mutumin ko mutuniyar da ta sayi dutsen ba, sabo da ta woyar tarho aka yi cinikin.
Jami’ai suka ce Azurfan wadda yake da siffar “Pear” shine mafi girma a wan nan launi a duk fadin Duniya.Girmansa kamar babbar tsayar hanu ta jinsin mace.
Kudin dutsen bai dara hasashe da kamfanin yayi, gabbanin a fara ciniki ba, kamfanin Sotheby yace sai tayu dutsen a sayeshi kan kudi da ya kama daga dala milyan 11-15.
A bara ne aka gano dutsen a Afirka ta kudu.