Yanzu dokar hana zirga zirgar zata fara ne daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe. An kafa dokar takaita zirga zirga da daren ne sakamakon tarzoma da wadansu suka yi ne makon da ya gabata, biyo bayan nada sabon sarkin Misau na goma sha daya Alhaji Ahmed Sulaiman.
Wadansu mazauna garin Misau da wakilin Sashen Hausa Abdulwahab Mohammed ya yi hira da su, sun bayyana cewa, an sami zaman lafiya da kwanciyar hankali yanzu, sabili da haka suka yi kira ga hukumomi su janye dokar hana zirga zirgar baki daya domin ba al’umma sukunin gudanar da ayyukansu da neman abinci.
Sun bayyana cewa, tuni sabon sarkin ya shiga fada, yana kuma karbar baki wanda ya kasance tabbacin zaman lafiya. Sun bayyanan cewa, talakawa suna ba jami’an tsaro cikakken goyon baya sabili da haka bai kamata a tauye hakinsu na walwala da neman abin kalaci ba.
Wakilin Sashen Hausa Abdulwahab Mohammed ya ruwaito cewa, jami’an tsaro sun kama mutane talatin da ake zargi da hannu a tarzomar da ta janyo kone konen ababan hawa da tayoyin mota a fadar sarkin da kuma manyan titunan garin Misau.
Ga cikakken rahoton da ya aiko mana daga Bauchi, Najeriya.