A yau Alhamis babbar kotun Sifaniya ta samu tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya Cif Luis Rubiales, da laifin aikata badala
Nan take kotun ta yanke masa hukunci tare da cin sa tara saboda sunbatar tauraruwar ‘yar wasan nan Jenni Hermosa a labbanta ba tare da son ranta ba.
An tuhume shi ne da laifin aikata badala tare da tursasawa kuma masu shigar da kara sun nemi a baiwa “Rubi” kamar yadda abokansa ke yi masa lakabi wa’adin zaman kurkuku na shekaru 2 da rabi.
Babbar kotun ta yanke masa tarar Yuro 10, 800 (kwatankwacin dala 11, 300) sai dai ta wanke shi daga zargin tursasawa akan zargin yiwa ‘yar wasar matsin lamba ta sassauta batun.
Rubiales, wanda ya musanta zargin aikata ba dai dai ba sannan ya shaida wa kotun cewar yana da yakinin cewar Hermoso ta amince da sunbatar.
Ya sauka daga jaorancin hukumar kwallon kafar a watan Satumban 2023, mukamin daya rike tsawon fiye da shekaru 5.
Dandalin Mu Tattauna