Jiya talata, an samu tashe-tashen hankula na fashewar bama-bamai tare da harbe-harbe da bindigogi a jihohi har uku a yankin arewacin Najeriya, yayin da lamarin rashin tsaro yake kara tabarbarewa ga al'ummar wannan yanki.
A Kano, an kai hare-hare da bama-bamai a kan ofisoshin 'yan sanda a Dala da Panshekara da kuma Gwauron Dutse a cikin birni da yammacin jiya. Idan ba a manta ba, an sha kai hare-haren da ba su yi nasara ba kan ofishin 'yan sanda na Dala. Har yanzu babu wani rahoto na irin hasarar rayukan da aka yi a nan Kano.
A Damaturun Jihar Yobe kuma, an kai wani sabon harin a karo na uku cikin mako guda a unguwar Sabon Pegi. Wakiliyarmu Saadatu Mohammed Fawu, ta yi hira da wani mazaunin unguwar ta Sabon Pegi a daidai lokacin da ake jin karar barin wuta da bindigogi a dab da gidansa.
Tashin Bam Da Harbe-Harbe A Damaturu Saadatu Tana Hira Da Wani Ana Ta Harbe-Harbe |
Har yanzu babu wani bayani da aka samu na rasa rai a Damaturun.
Su ma al'ummar garin Wukari a Jihar Taraba, sun fuskanci irin wannan mummunar ukuba ta tashin bam da harbe-harbe a dab da wani ofishin 'yan sanda dake garin. 'Yan sanda a Taraba, sun tabbatarwa da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz abkuwar wannan lamarin, amma sun ce har yanzu babu wani takamammen bayanin da suke da shi tun da cikin dare ne.
Wani mazaunin garin, ya bayyanawa Sashen hausa na Muryar Amurka irin abubuwan da suke gudana a lokacin.
Tashin Bam Da Harbe-Harbe A Wukari: Rahoton Ibrahim Abdulaziz |
Har yanzu babu wani ko wasu da suka dauki alhakin wadannan hare-haren, koda yake sun yi kama da na kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram.