Sama da mako guda kenan da al’ummar yankin Agbaji, suka shiga cikin wani yanayi na tashin hankali da firgici, sakamakon garkuwa da yara 8 da 'yan bindiga suka yi a wani gidan marayu tare da wasu magidanta 3.
An dai sake shiga cikin irin halin dimuwa bayan sako su, 'yan bindigar sun yi awon gaba da daya daga cikin wadanda suka kai kudin fansar yaran.
Mai magana da yawun 'yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Maryam Yusuf ce ta tabbatar da sako yaran masu kimanin shekaru 10 zuwa 13 tare da wasu magidanta 3, da aka yi awon gaba da su tun a ranar 23 ga watan Janairun da ya gabata a yankin na Agbaji.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wanda kuma aka harbe shi, kana aka yi awon gaba da matarsa, amma ya bukaci da a sakaya sunan sa, ya shaida wa Muryar Amurka cewa halin da ya tsinci kansa "gwamma ma a ce mutum ya mutu" don sun harbe shi, kuma suka bukaci matarshi ta bisu ko su kashe shi, daga baya ta bi su.
An dai sako yaran da safiyar ranar Lahadi da ta gabata, bayan biyan 'yan bindigar kudin fansa, sun sake tafiya da daya daga cikin wadanda suka yi namijin kokarin kai kudin, da kuma karbo yaran a wani kyauye dake kusa da jihar Kogi, duk kuwa da kudin da aka karba, lamarin da mazauna yankin su ka koka.
Ba sabon labari ba ne matsalar sace- sacen mutane domin karbar kudin fansa a Najeriya, inda rahotanni suka nuna cewa cikin makon da ya gabata kadai an yi garkuwa da kusan mutane dari a hare-haren da aka kai jihohin Kaduna, Naija, Katsina da Taraba.
Wani mazaunin yankin, ya bayyana halin rashin kwanciyar hankali da suke ciki, kana yana kiran gwamnati da ta dauki matakin da ya dace don kawo karshen wannan matsalar.
A yanzu haka babban birnin tarayyar kasar na fuskantar barazanar hakan. Kwamishinan 'yan sanda na birnin Abuja, Bala Ciroma, na cewa zasu kawo karshen irin waddannan miyagun ayyukan, don kuwa zasu kara yawan jami'ansu a duk lungu da sako da zummar hana su aikata irin wadannan ayyukan.
A halin da ake cikin an kubuto dukkan wadanda aka sace da farko a yankin na Agbaji, ana kuma cigaba da basu kulawa ta musamman. A cewar Ciroma.
Ga rahoton Shamsiyya Hamza Ibrahim daga Abuja, a cikin sauti.