Tawagogin ma'aikatan neman gawa sun gano gawarwaki dari da talatin da bakwai daga cikin mushen jirgin saman da ya fadi ranar Lahadi a wata unguwar birnin Lagos.
Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana kwanaki uku na makoki da juyayi da alhini. Ya ziyarci inda jirgin saman ya fadi kuma ya yi alkawarin cewa iri wannan bala'i ba zai sake faruwa, kuma ya sha alwashin daukan matakan kyautata hanyoyin kiyaye lafiyar zirga-zirgar jiragen sama.
Duka fasinjojin jirgin da ma'aikatan shi baki daya su dari da hamsin da uku sun mutu tare da wasu mutane a kasa wadanda ba a san adadin su ba.
Jim kadan kafin kafin jirgin saman ya fadi matukin jirgin ya sanar da cewa akwai wata matsalar inji. Amma jami'ai sun ce da sauran lokaci kafin a tabbatar da gaskiyar abun da ya haddasa hatsarin jirgin saman.